Wannan ne dai karo na biyu cikin makonni biyu a jere da rundunar tsaron Najeriya ke samun nasara kan 'yan bindiga da su ka hana manoma sukuni a jihar Kaduna da kuma wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
A makon da ya gabata, gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara ayyukan jami'an tsaro a dajin yankin Giwa, inda har aka hallaka jagoran 'yan bindigar yankin mai suna Buharin Yadi da sauran askarawan shi.
A ranar Juma'a kuma, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna malam Samuel Aruwan ya sake sanar da hallaka wasu 'yan bindigar daji, da ya ce bayanan sirri ne su ka tabbatar da cewa miyagun za su yi wani taro, abin da ya sa jami'an tsaro suka yi amfani da wannan damar su ka afka musu cikin dajin Yadi da ke yankin Giwa.
Ganin yadda aka cimma wadannan nasarorin a cikin makonni biyu ya sa masana harkokin tsaro irinsu Dr. Yahuza Ahmed Getso bayyana cewa da alama mahukunta sun fara gano laggon 'yan bindigar da su ka addabi arewacin Najeriya.
Sai dai kuma duk da haka masani kan harkokin tsaro Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce akwai bukatar jami'an tsaro su kara kaimi, inda ya jaddada bukatar a yi aiki na bai daya a dukkan jihohin da ke fama da hare haren 'yan bindiga.
Kafin wannan nasarar da aka samu, manoma a wasu yankunan jihar Kaduna sun fara kulla yarjejeniyar biyan kudin noma ga 'yan bindigar don samun izinin yin noma a bana, abin da ya sa wasu ke ganin akwai yuwuwar manoman su sami sauki idan ayyukan jami'an tsaro su ka dore.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:
Your browser doesn’t support HTML5