Jami’an Tsaro Da Mafarauta Sun Kubutar Da Mutane 39 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace

Wasu da ‘yan bindiga suka sake aka kubutar dasu

Rahotanni daga jihar Bauchi a Najeriya, na nuni da cewa wasu mutane 39 ‘yan asalin Duguri da ke yankin karamar hukumar Alkaleri da ‘yan bindiga suka sace a ranar Alhamis da ta gabata, a wani aikin sintiri na hadin gwiwar Jami’an tsaro da mafarauta.

BAUCHI, NIGERIA - Tawagar Gwamnan jihar Senata Bala Abdulkadir da kwamishinan ‘yan sanda, da daraktan hukumar DSS da Kwamandan Birged na Sojoji sun kai ziyarar jaje ga iyalai da kuma al’ummar kasar Duguri.

Wasu mata da ‘yan bindiga suka sace

Kwamared Bala Ibrahim Mahamud, Kantoman riko, na karamar hukumar Alkaleri, ya yi wa tawagar Gwamnan jihar da ta ziyarci garin na Duguri bayanin yadda aka gudanar da satar wadannan mutanen.

Wasu da aka kubutar da su daga hannun ‘yan bindiga

A nasa jawabin a madadin sauran jami’an tsaro, kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Auwal Musa Muhammad, ya yi bayanin yadda aka fafata da ‘yan bindigan da jami’an tsaro a maboyarsu.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad, ya bayyana murna da kuma yin gargadi ga duk wanda ke hada baki da ‘yan bindiga.

An ceto wasu mutane da ‘yan bindiga suka sace

Daga bisani daya daga cikin mutanen da aka kubutar da su, yayi bayanin yadda suka samu kansu kafin isowar jami’an tsaro, ya kuma bukaci gwamnatin jihar Bauchi da ta karfafa Sarkin Bakan Duguri da jama’arsa.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Abdulwahab:

Your browser doesn’t support HTML5

Jami’an Tsaro Da Masu Farauta Sun Kubutar Da Wasu Mutane Da ‘Yan Bindiga Suka Sace.mp3