Jami’an Kula Da Gidajen Gyara Halin Najeriya Sun Fito Da Wani Shirin Ilimantar Da Fursunoni 

Wani gidan gyara hali

Gidajen gyara hali a Najeriya, na ci gaba da kasancewa matattarar masu aikata laifuka mabambanta inda wasu masu laifi kan iya koyon wasu laifuka  na daban musamman wadanda ba su da aikin yi kafin a kai su kurkuku.

SOKOTO, NIGERIA - Domin rage irin wannan matsala ne ya sa jami'an kula da gidajen na gyara hali fitowa da shirye-shriye na koyawa fursunoni sana'o'i, kamar wani kawance da hukumar gyara hali ta kulla da hukumar koya rda sana'o'i ta NDE a Sokoto don koyar da sana'o'i ga fursunoni.

Mutanen da ake makawa da tuhumar aikata laifuka, sau da yawa ana turasu gidan gyara hali ne inda za su yi cudanya da wasu masu laifuka na daban.

Zaman jama'a wuri daya kamar na gidan gyara hali inda koda yaushe ana tare kan bayar da dama ga wasu matane daukar darasi daga wasu mai kyau ko munana.

Ibrahim Sani Ka'oje da ya taba yin kwamishinan ‘yan sanda a Sokoto a lokacin baya, ya ce wasu masu yunkurin garkuwa da mutane sun hada kai da wani fursuna lokacin da yake zaman kaso, abin da kan kara tabbatar da cewa ana iya koyon munanan dabi'u a gidan gyara hali musamman ga marasa aikin yi kafin shigar su wurin.

Hakan bai rasa nasaba da wani kawance da hukumar gyara hali a Sokoto ta shirya da hukumar koyar da aikin yi ga ‘yan Najeriya ta NDE ba don koyawa masu zaman kaso sana'o'i.

Kwantorolan hukumar gyara hali a Sokoto Aminu Yusuf ya ce sun lura cewa akasarin matsaloli da fursunoni ke fuskanta shi ne idan sun fito daga zaman kaso suna fama da rashin aikin yi har su sake aikata abubuwan da kan iya mayar da su.

A cewar shi, hakan ne ya sa suka yi tunanin idan sun hada kai da hukumar koyar da sana'o'i ta NDE su koyawa fursunoni sana'o'i za su samu sana'a idan sun fito su zama mutanen kirki wadanda ba zasu sake komawa ga aikata laifuka ba.

Jami’in hukumar koyar da sana'o'i Musamman Umar Sanda Gusau ya ce dama aikin su ne ganin sun samar da ayukkan yi ga ‘yan kasa domin sun gano cewa idan mutum bayi da aikin yi zuciyar shi na iya bugawa ya zama matsala ga kanshi da al'umma.

Ya ce kawancen da hukumar gyara hali zai yi alfanu domin idan gidan gyara hali sun gyara rayuwar fursuna su kuma zasu inganta rayuwar ta hanyar koya musu aikin yi.

Masu sharhi akan lamurran yau da kullum kamar Farfesa Tukur Muhammad Baba na ganin wannan kawancen abu ne da zai yi tasiri domin idan mutum ya samu aikin yi zai taimakawa kansa ya taimakawa kasarsa.

Akan haka ne masana ke ganin yana da kyau a karfafa wannan shirin ko da za'a samu raguwar zauna gari banza da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammadu Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Jami’an Kula Da Gidajen Gyara Halin Najeriya Sun Fito Da Wani Shirin Ilmantar Da Fussunoni .mp3