Kungiyoyin kasa da kasa irinsu Amnesty da Human Rigths Watch suma sun bayyana irin wannan damuwa game da halin da ‘yancin 'dan adam ke ciki a Nijar tun bayan da Janar Abdourahamane Tiani ya kwaci madafun ikon kasar.
A wata sanarwar da suka fitar a albarkacin ranar ‘yancin 'dan adam ta duniya kungiyoyin kare hakkin na 'dan adam membobin CODDH sun fara ne da bayyana gamsuwa kan wasu matakan da hukumomin kasar suka dauka kasancewar abu ne da ke kyautata rayuwar talaka injisu.
Sun bayyana cewa yakin da jami’an tsaro ke gwabzawa da ‘yan ta’adda wani abu ne da ta wani bangare ke zama silar tauye ‘yancin bil adama a Nijar.
Da yake jawabin a albarkacin wannan rana ministan shari’a da kare hakkin dan adam Mai Shari’a Alio Daouda ya bayyana cewa:
"A Nijar hukumomin koli a karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani tun a ranar 26 ga watan Yulin 2023 sun yi alkawarin bin hanyoyin karewa da bunkasa mahimman ‘yancin al’ummar kasar wadanda a halin yanzu da su ake dama komai da ya shafi jin dadin rayuwarsu."
Ya kuma kara da cewa bayan gudunmawar al’umma ya kamata dukkan kasashe da ofisoshi ko kungiyoyin gudanar da lamura su kasance masu kallon abubuwa da idanun adalci, su kuma mutunta ‘yancin kowace kasa game da abin da ta zabar wa kanta.
A jajibarin ranar ta ‘yancin 'dan adam Amnesty International da Human Rights Watch da hadakar OPDDH sun bayyana takaici a game da yadda hukumomin Nijar suka kama sakataren kungiyar AEC Moussa Tchangari cikin wani yanayin da ya saba wa doka, wanda kuma a ke tsare da shi a cibiyar yaki da ta’addanci a birnin Yamai a bisa zarginsa da wasu laifuka masu nasaba da ta’addanci.
Kungiyoyin na kasa da kasa sun yi kira a gaggauta sakinsa domin bita da kulli ake yi wa wannan dan gwagwarmaya kwatankwacin yadda ake yi wa ‘yan jarida da ‘yan fafutuka da ‘yan siyasa tun bayan juyin mulkin da Janar Tiani ya jagoranta inji su.
Ranar ta 10 ga watan Disamba ta zagayo ne a wani lokacin da jami’an fafutuka da ‘yan jarida da ‘yan siyasa ke cikin halin zullumi lamarin da CODDH ta ce ya saba wa alkawuran da hukumomi suka dauka a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yuli.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5