Bincike ya yi nuni da cewa, matsalolin kai hare-haren 'yan ta'adda da satar mutane domin neman kudin fansa, na daga cikin damuwowin da al'umar Jamhuriyar Nijar suka koka akai.
An bayyana hakan ne a taron sauraren korafe-korafen jama'a da kungiyoyi masu zaman kansu suka tattaro dangane da batun muzgunawar da suka ce sun fuskanta daga ‘yan bindiga ko kuma daga bangaren jami’an tsaro.
Andilo Mahaman Lawali darekta a hukumar kare hakkin dan adam ta Nijar ya ce sun tattauna kan matsalolin mutane musamman dauke-dauken jama'a domin neman kudin fansa tare da sarakuna da malamai domin a shawo kan wannan matsalar tsaron.
Yanzu haka yankuna akalla 4 daga cikin 8 na Nijar ne ke fama da hare-hare walau na ‘yan ta’adda ko na ‘yan fashi, matsalar da alamu ke nunin ta fara shafar sauran yankunan kasar.
Issia Manou na kungiyar kawadago ta CDTN na ganin taron ya zo akan daidai.
Samun sukunin zuwa da dawowa daga wannan gari zuwa wancan ko tsakanin yankuna biyu, na daga cikin muhimman ‘yancin da dokokin kasa da kasa suka yi tanadi domin bil’adama, saboda haka hukumar CNDH ke ganin bukatar daukar matakan gaggawa don bai wa jama’a damar morar wannan ‘yanci.
Bayanan da za su fito a karshen wannan taro na kwanki biyu na matsayin wani bangare na rahoton karshen shekara da kundin tsarin mulkin Nijar ya wajabtawa hukumar kare hakkin dan adam ta gabatarwa majalisar dokokin kasar kafin ta damka kwafinsa ga bangaren zartarwa domin nemo hanyoyin shafe hawayen al’umma game da batun ‘yancin dan adam.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Facebook Forum