Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakai Kan Bakin Haure A Nijar Baya Tasiri


Taron kasa da kasa kan bakin haure a Nijar
Taron kasa da kasa kan bakin haure a Nijar

Masu rajin kare hakkin bil'Adama a jamhuriyar Nijar sun ce dokokin da 'yan majalisar kasar suka dauka domin dakile kwararar bakin haure bayi tasiri ba.

Mahawarori na cigaba da zafafa tsakanin kungiyoyin dake fafutukar kare hakkin bil-Adam game da rashin tasirin dokokin da hukumomin kasar suka dauka da dokokin da majalisar kasar ta amince dashi a can baya domin dakile kwararar bakin haure a arewacin kasar ta Nijar.

A garin Durku,mahukunta sun tabbatar da ceton bakin haure tasa’in da biyu da jami’an tsaro dake sintiri suka yi da taimakon ayarin wata kungiya mai zaman kanta a iyaka da kasar Libiya.

Malam Jafaru, wani mai rajin kare hakkin dan Adam, yace dokokin da hukumomin kasar Nijar suka dauka gameda wannan lamarin sun kasa kai labarin, ganin cewa dokokin da hukumomin suka dauka sun takawa wasu birki akan wannan lamarin wasu cikin masu safaran mutane suna bullowa da wasu sabin dabaru.

Kasancewar Jamhuriyar Nijar mamba a kungiyoyi da dama a Afirka dake baiwa ;ya’yan nahiyar damar walwala a nahiyar yasa wasu ke ganin cewa bai kamata Nijar ta sabawa wannan doka ba idan har mutun ya cika ka’idoji.

Duk da daukan wadannan matakan har yanzu ‘ya’yan nahiyar ta Afika da dama ne ke saka rayukansu a cikin hadarin ko a mutu ko ayi rai kan batun tafiya kasashen turai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG