Abdullahi Mashi, suriki ne ga Mamu, ya na tsare a ofishin jami'an DSS da ke birnin tarayya Abuja a halin yanzu, a cewar 'yan uwansa.
Dan uwan Tukur Mamu, Elfarouq Mamu, ya shaida wa Muryar Amurka cewa jami'an tsaron sun kuma kai irin wannan samamen gidan kanin matar Tukur mai suna Ibrahim Tinja, wanda yake tare da Tukur a kasar Masar lokacin da aka tiso keyarsu zuwa Najeriya.
Tun da farko dai gidan Mallam Tukur jami'an tsaron suka fara kai samame da kuma gidan wani babban jami'i a kamfanin jaridarsa ta Desert Herald mai suna Ibrahijm Mada a daren ranar Laraba, inda suka yi awon gaba da wasu muhimman takardu, wayoyin salula da kwamfutoci.
'Yan uwan Mamun sun ce jami'an na DSS sun sako matan Tukur su biyu, amma har yanzu suna ci gaba da tsare da shi da babban dansa Faisal Mamu, da kanen matarsa Ibrahim Tinja.
A baya dai Tukur Mamu shi ya yi ta shiga tsakanin gwamnati da 'yan ta'adda don ganin an sako fasinjojin jirgin kasan nan da 'yan ISWAP su ka yi garkuwa da su a watan Maris na 2022.
Amma daga bisani ya bayyanawa VOA cewa ya janye daga aikin shiga tsakanin bayan da ya yi koken ana yi wa rayuwarsa barazana.