Wasu jami'an Amurka biyu sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters a ranar Talata cewa Amurka na shirin bayar da tallafin soji na dala biliyan 1 ga Ukraine, wanda shi ne na farko da za a samu daga kudirin dokar Ukraine da Isra'ila da ba a sanya wa hannu ba tukunna.
WASHINGTON, D. C. - Tallafin ya hada da motoci, makaman tsaron sararin sama na Stinger, karin harsasai na na'urorin roka na tafi-da-gidanka, harsasai na milimita 155, na'urorin yaki da tankokin yaki na TOW da Javelin da sauran makaman da za a iya amfani da su nan take a fagen daga, in ji jami'an da su ka yi magana bisa sharadin boye sunansa.
Shugaba Joe Biden dai ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta ba wa Ukraine taimakon dala biliyan 60.8, amma yunkurin ya ci tura yayin da ‘yan jam’iyyar Republican a majalisar wakilai suka ki amincewa da ci gaba da matakin na tsawon watanni.
-Reuters