Amurka ta dauki matakin tallafawa sojojin kasar Ukraine da miliyoyin daloli, kudaden da fadar White House ta hana sake su kafin wannan lokaci.
Jami’an fadar White House sun tabbatar a jiya Alhamis cewa an sake dala miliyan 250 daga asusun ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon da wani tallafi na karin dala miliyan 141 daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka, jim kadan kafin ‘yan majalisa su yi kashedi ga gwamnati.
Ma’aikatun harkokin kasashen waje da ta Tsaron Amurka za su ci gaba da aikin bada tallafin kudaden daga asusun sojoji da na tsaro ga Ukraine, a cewar wani babban jamai’in gwamnati.
Gwamnati tana taimaka wa Ukraine ne a kokarinta na kare kanta da kuma yin wasu sauye sauye, kana wadannan kudade za su taimaka wa Ukraine ta gudanar da wadannan ayyuka.
Facebook Forum