Kasashen biyar zasu karu da rukunin kasashe 15 na kwamitin sulhun wurin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, daga ranar daya ga watan Janairun shekarar 2020.
Ba a samu fargabar da aka saba samu a kan kuri’ar da aka kada a zauren Majalisar ba, inda yankuna suka zabi masu wakiltan su bada takara ba. A wannan shekarar, an tsayar da kasashen Tunisia da Jamhuriyar Nijer da Vietnam ba tare da wata fafatawa ba.
Kazalika kasar Saint Vincent and Grenadines, sai da ana dab da awa daya kafin kada kuri’ar ta jiya Juma’a ne, kasar El Salvador ta sanar da niyarta ta yin takara da karamar tsibirin a kan kujera daya tilo dake wakiltan yankin Latin Amurka da Caribbean.
Sai dai jami’an diplomaisy sun bayyana al’ajabin su kafin kada kuri’ar na shigar El Salvador takarar ana sauran ‘yan mintoci a yi zabe, yayin da yankin ya amince tun cikin watan Disemba za a gabatar da Saint Vincent a matsayin 'yar takara.