A yau Alhamis, Firam Ministan Denmark, Lars Lokke Rasmussen, ya sanar da cewa zai yi murabus, bayan da jam’iyyar adawar Social Democrats, ta lashe yawancin kujeru a zabukan da aka yi a kasar.
Jam'iyyar firam minister, Rasmussen ta Liberal, ta sami nasarar wasu kujerun, amma Jam'iyyar Danish Peoples Party, mai ra’ayin kishin kasa, da ta goyi bayan gwamnatin sa, ta sha kaye.
Jam’iyyar Social Democrat, ta samu kusan kuri’u kashi 26, cikin dari inda ta kasance a kan gaban duk sauran jam’iyyun kasar, abinda kuma zai ba Mette Frederiksen ‘yar shekaru 41 da haihuwa, damar zama firam Minista, mafi karancin shekaru da aka taba samu a kasar.
Facebook Forum