AGADEZ, NIGER - Bangarorin sun cimma wannan matsaya ce a ziyarar aiki da Shugaban gwamnatin, Nijar Lamine Zein, ya kai a kasashen a wani mataki na neman mafita ga takunkumin tattalin arziki da ECOWAS da kuma wasu kasashen duniya suka sanyawa kasar.
A yayin wata ziyara da Firai Ministan na Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine ya kai a kasashen na Iran da Turkiya ne suka kulla yarjejeniyar tsaro da kara inganta hulda ta fannonin ci gaba da dama a tsakanin kasashen.
Tawagar Firai Ministan dai ta kunshi Ministoci shida da suka hada da na tsaro da man fetir da na noma da kuma kasuwanci.
Makasudin wannan ziyarar dai ita ce kokarin samar wa kasar Nijar mafita daga takunkuman kasashen Africa ta yamma da ECOWAS wanda suka kakaba mata, matakin da yakai ga kulla yarjejeniyar kasuwanci da wadannan kasashen a cewar Firai Ministan Nijar, Ali Lamine Zaine.
Masana irin su Alkassoum Mato na ganin akwai bukatar Nijar ta inganta huldarta da sabbin kasashe irin su Tukiya da Iran.
Yanzu dai ‘yan kasar Nijar sun zura ido su ga sakamakon wannan yarjejeniya daga gwamnatin wadannan kasashe wajen taimakawa Nijar fita daga cikin matsalolin da take fuskanta sakamakon takunkuman tattalin arziki da kasashen Afirka ta yamma suka saka mata bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar da ta gabata, tun daga bayan juyin mulki da kuma raba gari da kasar Faransa.
Al’umma a Nijar da dama sun bayyana fatan ganin kasar su ta karfafa huldarta da kasashen Rasha da turkiya da kuma Iran, musamman a fannin tsaro.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Your browser doesn’t support HTML5