James Comey Zai Bayar Da Bahasi Gaban Majalisar Dattawan Amurka

Tsohon shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, James Comey.

Yau Alhamis din nan tsohon shugaban hukumar binciken aikatta laifuffuka ta FBI James Comey da shugaba Trump ya kora zai yiwa kwamitin leken asiri na Majalisar Dattijan Amirka bayanin cewa shugaba Trump ya bukaci ya yi masa biyayya.

Shugaban yayi wannan bukata ce a wata tattaunawa da suka yi a fadar shugaban Amirka ta White House dangane da yadda hukumar FBI take binciken jami’an gwamnati na da dana yanzu.

Ana sa ran bahasin da Mr Comey zai gabatar ya baiyana dalla-dallar tattaunawa sau biyar da yayi da shugaba Donald Trump wanda a lokacin shugaban na Amirka ya bukaci Mr Comey daya canja akalar binciken da hukumar FBI take yi.

A wani labarin kuma, jiya Laraba Shugaban Donald Trump ya zabi Christoper Wray a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon shugaban hukumar binciken aikata laifuka ta FBI, James Comey.

Mai magana da yawur fadar shugaban Amirka Sarah Hukabee Sanders ta fada a jiya Laraba cewa shugaba Trump ya zabi Mr Wray a saboda irin aiyukan da yi, da kuma goyon bayan da yake dashi na dukkan jam’iyun Amirka.