'Yan Jam’iyyar Democrat sun karbe ikon Majalisar Dattawan Amurka, lokacin da mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris ta rantsar da sabbin mambobi uku don baiwa jam’iyyar ‘yar tazara a Majalisun biyu da kuma fadar White House a karon farko cikin shekaru goma.
Sanata Raphael Warnock, da Jon Ossiff daga jihar Georgia, da Alex Padilla daga jihar California, sun karbi rantsuwar kama aiki, ‘yan sa’o’i bayan da aka rantsar da Biden.
Sanata Warnock da Ossoff, sun lashe zaben su ne a zagaye na biyu na zaben da aka yi a ranar biyar ga wannan watan na Janairu, zaben na su yasa Majalisar ta rabu diga biyu kowace jam’iyya na da mambobi 50.
Shi kuwa Sanata Padilla, an nada shi ne don ya maye gurbin mataimakiyar shugaban kasa Kamala, wadda ta ajiye aikin ta a ranar Litinin, aka kuma rantsar da ita jiya a matsayin mataimakiyar shugaban kasa.