ABUJA, NIGERIA - Jam’iyyar dai ta dau matakin ne a ranar karshe ta mika sunayen ‘yan takara na shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya ga hukumar zabe INEC.
Majiyoyi masu tushe daga gidan dan takarar Tinubu da helkwatar APC na tabbatar da mika sunayen Tinubu da Masari amma ba tare da amincewa su bayyana hakan ta nadar sautinsu ba.
Duk bayanan na nuna tsohon sakataren walwala na APC Kabir Ibrahim Masari ya zama mataimakin don cika ka’idar hukumar zabe ta mika sunan dan takara da mataimaki, amma daga bisani za a yi amfani da damar sauya dan takara da hukumar zabe za ta ayyana lokacin karba da rufewa.
Kakarewar tsaida dan takarar mataimakin don muhawarar addini da yankin da zai fito a yankuna uku na Arewa ta haddasa wannan takaddama.
Mamba a kwamitin kamfen din Tinubu, Barayan Bauchi Sunusi Baban Takko ya tabbatar da mika sunan amma ya kaucewa karin bayani kan mataimaki da muradinsu na yin hakan.
A bangaren ‘yan majalisar dattawa ma za a iya samun irin wannan sauya sunan don wasu manyan ‘yan majalisa sun gaza samun tikitin takara irin shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, tsohon gwamna Godswill Akpabio da kuma Sanata Adamu Aliero a mazabar Kebbi ta tsakiya da ya sauya sheka zuwa PDP.
Haruna Dan D.O Saidu wanda ya lashe takarar Sanata a Kebbi ta tsakiya a inuwar PDP ya ce ba zai sauka daga takarar ba.
Yanzu idanu sun koma mika sunayen ‘yan takarar gwamna da ‘yan majalisar jiha ga hukumar zaben zuwa 15 ga watan gobe.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5