Yayinda a dai gefe guda kuwa an hana jama’a morar ‘yancin gudanar da zanga zanga.
Lamarin da jam’iyar ta ADR tace ba za ta zuba ido ta na kallo ana yi wa talakawa kama karya ba sai dai wani kakakin jam’iyar PNDS mai mulki na kallon abin tamkar wani korafi irin na ‘yan adawa.
A yayin gangamin da ta shirya a albarkacin cika shekaru 2 da shigowarta fagen siyasar Nijer jam’iyar ADR Mahita ta dan takara a zagayen farko na zaben shugaban kasa na watan disambar 2020 Ousman Idi Ango Sadauki ta yi bitar halin da ake ciki a wannan kasa watanni 18 bayan da shugaba Mohamed Bazoum ya haye karaga mulki.
Mamba a kawancen jam’iyun adawa na CAP 20 21 da ACC jam’iyar ADR Mahita ta nuna takaicinta akan yadda rayuwa ke kara yi wa tallaka wuya a wanna kasa kamar yadda babban magatakardanta Alhaji Aboubacar Ma’azou mai lakanin Ambouka ya bayyana.
Rashin mutunta mahimman ‘yancin da dimokradiya ta yi tanadi wa ‘yan kasa na daga cikin matsalolin da jam’iyar Mahita tace sun ta’azzara a wannan zamani na gwamnatin PNDS Tarayya.
Shugabanin jam’iyar sun lashi takobin ci gaba da fafutikar ganin an bai wa ‘yan kasa hakkokinsu.
Sai dai kakakin jam’iyar PNDS Alhaji Assoumana Mahamadou na cewa wadanan zarge zarge ba su da tushe.
ADR Mahita wace aka kafa a watan satumban 2020 bayan da wani sabani ya kunno kai a tsakanin shugabanin jam’iyar PNDS da a dai bangare wani jigonta wato jagoran matasan jihar Tahoua Idi Ango Ousman Sadauki ta shiga babban zaben Nijer na 2020 abinda ya ba ta damar samun wakilai a majalisun karkara haka kuma ta na daga cikin jam’iyun dake da kujerun wakilci a majalissar dokokin kasa.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5