Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Ta Caccaki Rasha Akan Syria

Shugaban Syria Bashir al-Assad ( a hagu) da Shugaban Rasha Putin (a dama) yayinda shugaban Syrian ya kai ziyara Moscow

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Powel ta yi kaca-kaca da Rasha akan shiganta yakin Syria.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta yi kaca-kaca da maganar kutsen sojojin Rasha a Syria da sunan shiga tsakani.

Tace hakan ya ma karawa ISIS karfi ne ta wajen sake samun damar ikon kwace karin wasu wurare.

Samantha Powel tace, hare-haren saman Rasha da ta fara a ranar 30 ga watan Satumbar da ya kamata na taimakawa shugaban Syria ne tare da tabbatar da cewa ya cigaba da mulkin danniya da yake yi.

Ba komai ya karawa matsalar ba face dakushe kaifin ayyukan da ake yi tare da maida hankalin karya lagon ISIS

Power tace, shigar Rasha yakin ya ma karawa ISIS karfi ne, saboda yawan kai hare hare da ake yi akan jama’ar da ba ‘yan ta’adda bane.

Kamar yadda kungiyar ‘Yan Syria mai rajin kare ‘yancin bil’adama ta ruwaito yadda hare-haren Rasha yak e fadawa kan makarantu da kasuwanni a yankin Aleppo.

Sannan harin ya hallaka mutane akalla guda 100.

Majalisar Dinkin Duniya tace, sabon harin na Rasha ya raba mazauna yankin Aleppo daga Kudancin kasar tare da wasu kuma kimanin 35,000 daga Hama. Gaba daya akalla mutane 85, 000 ko ma fiye suka rasa muhallansu tun lokacin da Rasha ta fara kai hare-hare da jiragenta.