Jami’an rundunar sojojin Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawarsu karo na uku don fayyace dokoki da ka’idojin sararin samaniyar Syria.
Domin samin daidaiton fahimtar dokokin salama wajen aiwatar da ayyukansu da nufin gujewa hatsarin karon battar da ba a yi niyya ba.
Ma’aikatar tsaron Amurka tace, an sami ci gaba a taron tattaunawar da ya gudana ta hanyar sadarwar bidiyo ta yanar gizo a jiya Laraba.
Wanda tattaunawar ta maida hankali ne kacokan a game da matakan kare lafiya ta wajen kaucewa arangama.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, taron ya maida hankali wajen fidda daftarin matsayarsu a nan gaba.
Dukkan bangarorin kasashen biyu sun yarda da cewa, an yi tattaunawar bisa kwarewar aiki, sannan gab ake da cimma yarjejeniya.