Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Saman Yakin Amurka da Rasha Sun Kusa Karo da Juna a Syria


Sakataren Tsaron Amurka Ashton Carter
Sakataren Tsaron Amurka Ashton Carter

Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter yace yana fatan za'a cimma yarjejeniyar cikin dan karamin lokaci tsakanin Amurka da Rasha kan tabbatar lafiyar jirage da matukansu a sararin samaniyar Syria, domin kaucewa hadari tsakaninsu.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta fada jiya Talata cewa a makon jiya jiragen yakin kasashen biyu sun zo kusa da juna inda kilomita 16 ne kacal suka raba tsakaninsu, har matuka jiragen suna iya karanta lambobin da aka rubuta akan jiragen.

Duk da cewa muna ci gaba da jayayya da kan manufofi gameda Syria, akalla zamu iya cimma yarjejeniya na tabbatar da lafiyar matuka da jiragensu" inji Sakatare Carter a wani taro da manema labarai a Boston jiya Talata. Tilas Rasha ta gudanar da ayyukanta a sararin Syria da kwarewa, kuma ta mutunta sharuddan kiyaye lafiya.

Daga bisani kakakin ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon, Peter Cook, yace jami'an ma'aikatar zasu tattauna d a takwarorinsu na Rasha ta bidiyo. Tattaunawar zata fi maida hankali ne kan sharuddan kiyaye lafiya na matuka jiragen saman yaki da kayan aikinsu.

Sakatare Carter yace Amurka ba zata canza shirinta na ci gaba da kai farmaki kan kungiyar mayakan sakai ta ISIS a Syria b. Duk da haka yayi kira ga Rasha tayi watsi da shirinta "wanda bashi da karko", wanda yace ba zai haifi da mai ido ba, wanda kuma bashi da hangen nesa ko kiyaye abun da ka faru nan gaba.

XS
SM
MD
LG