Khamenei yace yan Saudia marasa tausayi masu kashe bayin Allah sun hada wadanda suka mutu da masu rauni a wuri daya a maimakon a basu magani ayi musu jinya ko kila za’a cetosu. Yace su suka kashesu. Khamenei yayi wa’yanna kalaman ne a wata sanarwa da ya dora akan shafinsa na yanar gizo, na cika shekara daya da faruwar wannan bala’i. Sai dai bai bada wata shaida ba akan zargin da yayi.
Nan take Saudiya ta mayar mai da martini, inda Yarima mai kula da harkokin cikin gida Mohammed bin Nayef, yace Iran tana kokarin sa siyasa acikin harkar haji da ake bukatar akalla kowane musulmi ya samu a cikin rayuwarsa.
A cewar gwamnatin Sadia turmutsumutsun na bara yayi sanadiyar mutuwar mutane 769, to amma kampanin dillacin Labarai na AP tace yawan mutanen da suka rasa rayukkansu a cikin hargitsin sun kai mutane dubu biyu da dari hudu da 26 bayan ta tattara jawaban da wasu kafofin yada labarai na cikin da jami’ai da yan kasashensu suka je haji.
Ita kuwa gwamnatin Iran tace mutane 464 da suka mutu duk Iraniyawa ne kuma sun dora laifin wannan bala’i a kan gazawar gwamnatin Saudia.