Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Saudiya Ta Tanadi Bada Cikakken Tsaro Lokacin Aikin Hajjin Bana


Masallacin Annabi Muhammad (SAW) dake Medina wanda aka taba kaiwa hari
Masallacin Annabi Muhammad (SAW) dake Medina wanda aka taba kaiwa hari

Mahukuntan Saudiya sun samar da sabbin motocin tsaro irin na zamani dubu ukku tare da jami'an tsaro dubu goma sha bakwai a lokacin aikin hajjin bana da za'a fara mako mai zuwa

Kwamandan jami'an tsaron farin kaya na kasar Manjo Janar Hamad bn Abdulaziz si ya sanar da hakan yau Litinin.

Yace jami'an tsaron sun shirya tsaf domin bada duk wata kariya ga alhazai a lokacin gudanar da aikin hajji.

Masu nazari akan alamuran tsaro na ganin matakin ya dace.bisa ga la'akari da yadda kasar ke kara fuskantar kalubalen tsaro. Ko a gwanakin baya an samu tashin bamabamai a kasar da suka hallaka jama'a.

Ministan Tsaron Saudiya Mohammad bin Salman Al Saud
Ministan Tsaron Saudiya Mohammad bin Salman Al Saud

A cikin wuraren da aka kaiwa hari har da masallacin Annabi Muhammad (SAW) dake birnin Medina.

Alhaji Musa Suleiman dake kula da harkokin tsaro na kasa da kasa da yake aikin hajjin bana daga Najeriya yace hakika Saudiya tayi rawar gani wajen samo sabbin motocin tsaro. Yana goyon bayan matakan tsaro da kasar ta dauka.

Ga rahoton Nasiru Batsari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG