Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Amurka Suyi Magana da Murya Daya Akan Madaidaicin Albashi - Obama


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce idan ma’aikata suka yi magana da muryar daya kan batun albashi madaidaici da kuma neman wa kansu mutunci a wuraren aikinsu, hakan su na ba da labari ne kan yadda Amurka ta ke.

Obama ya bayyana hakan ne a yau Litinin a wata budaddiyar wasika da ya aikawa ma’aikatan kasar yayin da ake bikin ranar ma’aikata a nan Amurka.

Ranar ta ma’aikata, wacce ta kasance hutu ne a duk fadin Amurka, ta samo asali ne tun daga shekarar alif dari takwar da casa’in da hudu (1894), akan kuma yi bikin ne a Litinin din farkon kowane watan Satumba.

Shugaban na Amurka ya kara da cewa, a yau da ace, ya na neman aiki, wanda zai yi domin sama wa iyalansa tsaro, da ya shiga kungiyar ‘yan kwadago.

Obama ya ce tarihi ya nuna cewa ma’aikata za su iya cimma burinsu, amma fa idan suka hada kansu wuri guda suka yi fafutukar neman wa kansu ‘yan ci.

XS
SM
MD
LG