Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Rasha Sun Kasa Cimma Daidaito Kan Tsagaita Wuta A Siriya


John Kerry da Serge Lavrov sakatarorin harkokin wajen Amurka da Rasha
John Kerry da Serge Lavrov sakatarorin harkokin wajen Amurka da Rasha

Sakatren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaran aikinsa na Rasha, Sergie Lavrov, sun kasa cimma matsaya a karo na biyu a jere a yau Litinin, kan yadda za a cimma shirin tsagaita wuta a Syria, wanda hakan zai iya ba da damar gudanar da ayyukan jin-kai, ga mutanen da yakin na Syria ya daidaita

Manyan jami’an diplomisayyar biyu, sun hadu ne a Hangzhou, da ke kasar China, inda shugabannin kasashen duniya 20 da suka fi karfin tattalin arziki ke taro kolinsu.

Shi dai shirin na tsagaita wuta da ake so a cimma, sai ya hada da gwamnatin Syria wacce kawa ce ga Rasha da kuma ‘yan tawayen da Amurka ke marawa baya, idan har ana so a kaiwa miliyoyin ‘yan kasar ta Syria daukin kayayyakin abinci da na magunguna.

A kuma gefen taron Shugaban Amurka Barack Obama da takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin, sun yi wata ganawa a yau Litinin, sai dai babu wasu bayanai da suka fito daga wannan taro.

Amma dai ga dukkan alamu, kasashen biyu na yunkuri ne su ga cewa sun samu matsaya guda, amma kuma akwai alamun an dan samu tarnaki.

A jiya Lahadi dai shugaba Obama ya ce, akwai banbancin ra’ayi kan bangarorin da Amurka da Rashan ke marawa baya da kuma matakan da za a bi domin samar da zaman lafiya a kasar ta Syria.

XS
SM
MD
LG