Domin bunkasa harkokin ilimi da kimiyya da fasaha a fadin Nahiyar Afirka, gidauniyar bada ilimi da aka yiwa lakabi da Rochas and Zuma foundation, sun kulla yarjejeniya domin tabbatar da horas da dalibai marasa galihu guda biyar daga kowace kasa a nahiyar Afirka.
Shugaban kasarAfirka ta kudu Jacob Zuma, da gwamnar jihar Imo, Rochas Okorocha ne suka rattaba hannu akan wannan yarjejeniyar a ranar Asabar a harabar Rochas foundation dake Owerri, babban birnin jihar.
Dr Ebere Nzewuji, shine mai taimakawa gwamna Rochas Okorocha, wajan fannin yada labarai, ya bayyana cewa gwamna Rochas ya ziyarci kasashen Afirka 55, daga inda ya dauki yara biyar daga kowace kasa domin basu irin wannan tallafin, lamarin da ya janyi hankalin jama'a da alfarma mai dinbin yawa.
Ya kara da cewa a nan gida Najeriya kuma, gwamnan ya fi mayar da hankali ne wajan tallafawa 'ya'yan gajiyayyu da mataulauta wajan tabbatar da basu ilimin zamani kyauta, ta hanyar aiki kafada da kafada da shugabannin kasashen domin tantance sharuddan daukar yaran.
Bayan sun kammala rattaba hannun ne gwamnatin jihar ta karrama shugaba Jecob Zuma da lambar yabo mafi martaba a jihar da aka yiwa lakabi da Grand Chancelor of Imo State, a dandalin Heroes past dake babban birin jihar.
Rochas Okorocha ya bayyana dalilin yin hakan a matsayin nuna godiya ga shugaban na Afirka ta kudu musamman yadda yake nuna goyon bayan inganta ilimin zamani duk da cewa shi bai same shi ba, amma gashi yana yunkurin ganin kowane dan talaka ya ilimantu.
Saurari rahoton Alphonsus Okoroigwe domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5