Babu Zancen Daunin Iko A Ivory Coast

Sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daga Nijar,suke sintiri suna wucewa kusa da hoton Alassane Ouattara.

Mai shiga tsakani da sunan kungiyar kasashen Afirka, Raila Odinga, ya fada a jiya talata cewa dole ne wanda ya sha kaye a zabe, ya karbi hukuncin jama’a.

Masu magana da yawun kungiyar kasashen Afirka da gwamnatin kasar Amurka sun ce yin daunin iko ba zai warware rikicin siyasar kasar Cote D’Ivoire ba.

Mai shiga tsakani da sunan kungiyar kasashen Afirka, Raila Odinga, ya fada a jiya talata cewa dole ne wanda ya sha kaye a zabe, ya karbi hukuncin jama’a.

A wani lamari na daban, shi ma kakakin ma’aikatar harakokin wajen Amurka, PJ Crowley ya ce dole ne shugaba Laurent Gbagbo ya yarda ya sha kaye a zabe kuma ya mika mulki.

Wani kakakin shugaba Gbagbo ya gayawa sashen Faransancin Muryar Amurka cewa shugaban ya gabatarwa da kungiyar kasashen yammacin Afirkata ECOWAS, bukatar shi ta neman a sake kidaya kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar da aka yi a cikin watan nuwamba.

Mr.Gbagbo dai ya kafe akan cewa shi ne ya yi nasara a zaben kuma ya ki ya mika mulki.

Kungiyar ECOWAS/CEDEAO ta fada a can baya cewa Mr. Gbagbo ya yarda a tattauna yadda za a kawo karshen rikicin cikin lumana, amma ba tare da gitta wasu sharudan share fage ba. Haka kuma kungiyar ta ECOWAS ta ce ya yi alkawarin kawar da shingen da ke kewaye da otel din da abokin jayayyar siyasar shi Alassane Ouattara ya ke ciki a birnin Abidjan.

Sanarwar ta ECOWAS ta bayyana cewa Mr.Ouattara zai tabbatar da cewa Mr.Gbagbo ya bar mulki cikin mutunci idan ya yarda da kaddarar cewa ya sha kaye a zabe.