Isra’ila Za Ta Mika Wa Amurka Gaza Bayan Lafawar Rikici - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump

A yau Alhamis Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar Isra’ila zata mikawa kasarsa iko da Gaza bayan lafawar rikici tare da tsugunar da al’ummar zirin a wani wuri na daban, abinda yace ba zai bukaci tura dakarun sojin Amurka zuwa yankin ba.

Kwana guda bayan da sanarwar da Trump yayi ta cewar yana da niyar karbe iko da zirin Gaza tare da mayar da shi dausayi a gabas ta tsakiya, Isra’ila ta umarci rundunar sojinta data shirya kyale mazauna Gazan dake son ficewa bisa raddin kansu su wuce.

Trump, wanda a baya yaki ya janye batun tura sojojin Amurka zuwa Gaza, ya fayyace shirin nasa a kalaman daya wallafa a shafin sada zumuntarsa na “Truth Social Web”.

“Bayan lafawar rikici Isra’ila zata mikawa Amurka zirin gaza,” a cewarsa. kannan an sake tsugunar da Falasdinawa a amintattu kuma garuruwa mafi kyau, a cikin sabbin gidaje na zamani, a yankin.”

“Ba za’a bukaci sojan Amurka ko guda ba!” a cewarsa.

Tunda fari Ministan Tsaron Isra’ila yace ya umarci rundunar sojin kasar ta fara tsare-tsaren barin Falasdiwan dake burin ficewa daga zirin Gaza bisa raddin kansu suyi hakan.

Amma duk da haka mazauna yankin sun ce sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na shirin kwace yankin da kuma korar su ya sanya su kara azama wajen ci gaba da zama.

-Reuters