Isra'ila Ta Lashi Takobin Dannawa Zuwa Yankin Kudancin Gaza, Yayin Da Ake Tattaunawar Sulhu

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Firai Ministan Isra'ila ya fada a ranar Lahadi cewa, yuwuwar tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da mayakan Hamas zai jinkirta kai hari ta kasa ne kawai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda ya zama mafaka ga fiye da rabin al'ummar yankin da ke fuskantar rikici.

A yayin da ake fama da matsalar jin kai, babbar hukumar ba da agaji ga Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a dauki matakan siyasa don dakile yunwa a Gaza.

Masana daga kasashen Masar, Qatar da Amurka sun gana a birnin Doha, har ma da wakilan Isra'ila da na Hamas, kamar yadda kafafen yada labaran Masar masu alaka da gwamnatin Masar suka bayyana, wani kokari na baya-baya da ake don ganin an cimma yarjejeniya kafin watan Ramadana mai alfarma.

Firai Minista Benjamin Netanyahu ya ce farmakin soji a Rafah da ke kan iyakar Gaza da Masar, zai taimaka wa Isra'ila samun "cikakkiyar nasara" cikin ‘yan makwanni akan Hamas, mayakan da harin da suka kai a ranar 7 ga watan Oktoba ne ya ya yi sanadiyar fara yakin.

Ana fargabar irin wannan farmakin zai janyo asarar rayukan fararen hula da yawa a Rafah, inda Falasdinawa kusan miliyan 1.4, wadanda akasarinsu ‘yan gudun hijira ne daga wasu wurare, suka tattaru.

"Ko da ba mu cimma wata yarjejeniya ba, za mu cigaba da yin hakan," in ji Netanyahu.

"Dole ne a yi hakan domin cikakkiyar nasara ita ce burinmu, kuma tana gab da samuwa - ba nan da watanni ba, amma nan da makonni kadan da zarar muka fara aikin," abinda Netanyahu ya gaya wa CBS kenan game da kai farmaki ta kasa.

Mummunan karancin abinci da ake fama da shi a arewacin Gaza wanda ya sa Falasdinawa tserewa zuwa kudu "wani bala'I ne bil’adama ya janyo wanda za a iya shawo kan lamarin," in ji Philippe Lazzarini, shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNRWA.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana fuskantar kalubale musamman akan kai kayan agaji zuwa arewacin Gaza.

Wata majiyar Hamas ta shaida wa AFP cewa, an gabatar da wasu sabbin gyare-gyare kan batutuwan da ake takaddama a kai, amma Isra'ila ba ta gabatar da wata kwakkwarar matsaya ba akan sharuddan tsagaita wuta da kuma janyewa daga zirin Gaza.

Netanyahu ya yi watsi da bukatar janye sojojinsa.

Sama da watanni hudu da aka kwashe ana yakin, akan dole iyalai marasa galihu a arewacin Gaza suke neman abinci a bola saboda fada da warwaso sun dakatar da kai kayan agaji.