Isra'ila Ta Ki Amincewa Da Tayin Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Hezbollah

Netanyahu

A yau Alhamis, Isra’ila ta yi fatali da shawarar tsagaita wuta tsakaninta da Hezbollah, inda ta bijirewa kawayenta ciki har da Amurka da suka bukaci a dakatar da yaki nan take na tsawon makonni uku domin bada damar yin amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen kaucewa fadadar yakin

“Ba za’a samu tsagaita wuta a yankin arewaci ba, “a cewar sakon da Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Isreal Katz a shafinsa na X, inda ya wallafa cewa, zamu ci gaba da yakar kungiyar ‘yan ta’addar Hezbollah da dukkanin karfinmu har sai mun samu nasarar mayar da mazauna yankin arewacin kasarmu gidajensu.”

Najib Mikati

Kalaman nasa sun rushe fatan da ake da shi na samun maslaha cikin sauri, bayan da Firai Ministan Lebanon Najib Mikati ya bayyana fatan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar nan ba da jimawa ba, inda dubban daruruwan mutane suka arce daga gidajensu domin neman tsira.

Shugabannin duniya sun bayyana damuwa game da rikicin-wanda ke gudana lokaci guda tare da yakin zirin gaza-kuma ke kazancewa cikin sauri.

Amos Hochstein - Najib Mikati

Fada mafi muni cikin shekaru 20 da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da kungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan kasar Iran ya sanya fargaba game da sabon samamen Isra’ila ta kasa a yankin kan iyakokin kasar da Lebanon.

-Reuters