Isra'ila Ta Kara Karfin Dakarunta A Lebanon Bayan Harin Da Iran Ta Kai Mata

APTOPIX Israel -ebanon

A yau Laraba, rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewar dakarun sojin kasanta dana motocin sulke zasu shiga cikin samamen da take kaiwa yankin kudancin Lebanon domin zafafa hare-haren da take kaiwa kungiyar Hizbullahi

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ilar ke shirin kai harin ramuwar gayya kan dimbin hare-haren makami mai linzami da Iran ta kai mata.

Bayan yakin da take fafatawa da kungiyar Hamas a Gaza, Isra’ila na kara yawan dakarunta a kudancin Lebanon a yakin da take yi da Hizbullahi kwana guda bayan harin da Iran ta kai mata, abinda ke kara fargabar cewar yankin Gabas ta Tsakiya mai arzikin man fetur na iya kara fadawa cikin karin rikici.

Karin dakarun sojin kasa da rundunar sojin sulke ta 36, ciki harda burged din Golani, da burged din sojojin sulke ta 188 da takwararta sojin kasa ta 6, na nuna cewar yakin ya kara zafafa.

Rundunar sojin tace manufar yakin ta kasa shine lalata hanyoyin karkashin kasa da gine-ginen dake kan iyaka amma babu shirin fadada kai hare-haren zuwa Beirut ko wasu manyan biranen dake kudancin Lebanon.

-Reuters