A yau dakarun Isra’ila suka ce sun sake kashe wani babban jami’in Hezbollah a wani hari ta sama, a daidai lokacin da kungiyar dake Lebanon ke cikin juyayin kisan shugaban ta Sayyadi Hassan Nasrallah.
Sojojin Isra’ilan sunce sun kashe mataimakin shugaban majalisar gudanarwar Hezbollah Nabil Kaouk a ranar Asabar. Anan take dai ba’aji wani furuci ba daga Hezbollah ba, kuma ba a san takamaiman wurin da aka kai harin na baya bayan nan ba.
A yan makonnin nan dai, hare haren Isra’ila ya yi ajalin kwamandojin Hezbollah da dama, da ya hada da manbobin kungiyar da ke da kusanci da Nasrallah, da suka kwashe gwamman shekaru suna tsallake tarkon mutuwar da aka rika dana mu su.
Haka zalika, an sha kaikaitar kungiyar ta Hezbollah da giggan hare hare ta na’urorin sadarwar ta, da na aikewa da sakonni da aka dora alhakin su a kan Isra’ila. Hare hare da dama da Isra’ila ta rika kaiwa a sassan Lebanon da dama, ya kashe mutane akalla dubu 1 da 30, da ya hada da mata su 156 da yara 87, duk a cikin kasa da makonni biyu, cewar ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon.
Dubban daruruwan mutane ne hare haren da Isra’ila ta rika kaiwa a kwanan nan ya kora da ga gidajen su a Lebanon. Gwamnati ta kiyasta cewa, kimanin mutane dubu dari biyu da hamsin aka tsugunnar, inda wasu da suka ninka adadin sau uku zuwa hudu su ka rabu a wurin yan’uwa da abokai ko suka samu mafaka a gefen tituna, kamar dai yadda ministan muhalli Nasser Yassin, ya shaidawa kafar labarum Associate Press.
Hezbollah ta cigaba da harba rokoki da makamai masu linzami kan Arewacin Isra’ila, duk da dai an harbo da dama da ga ciki, wasu kuma suka rika fadawa kasa, da ya raunata yan tsirarun mutane da barnar da bata taka kara ta karya ba.
Kaouk dai wani tsohon mamban Hezbollah ne tun a shekarun 1980 da ya taba zama kwamandan sojin Hezbollah a kudancin Lebanon a yayin yakin da ta gwabza da Isra’ila a shekarar 2006. A lokacin an rika ganin shi a kafar yada labarun kasar a kai akai, yana magana a kan siyasa da cigaban tsaro, tare da yin adduo’i a lokuttan janazar manyan mayakan kungiyar. A shekarar 2020 Amurka ta sanar da kakaba ma shi takunkumai.
Dandalin Mu Tattauna