Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a tashar jiragen ruwa ta Hodeidah a Yeman wadda ke karkashin ikon 'yan tawayen Houthi ranar Asabar, kwana daya bayan da wani harin jirgin sama mara matuki da 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Iran suka kai ya yi sanadin kisan farar hula daya a Tel Aviv, kamar yadda bangarorin biyu suka bayyana.
Hare-haren da suka haddasa tashin gobara da kuma turnukewar bakin hayaki, su ne na farko da Isra'ila ta dauki alhakin kaiwa a mashigin kasar mafi talauci a yankin kasashen Larabawa, mai tazarar kilomita 2,000, daga wurin, a cewar manazarta.
"Zubar da jinin 'yan Isra'ila zai janyo mummunan sakamako," a cewar ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant, ya kara da cewa zasu kai karin hare-hare kan 'yan Houthi nan gaba "idan ‘yan tawayen suka kuskura suka kai musu hari."
Gallant ya ce harin na Hodeida kuma na zaman gargadi ga sauran kungiyoyin mayakan da ke samun goyon bayan Iran a yankin Gabas ta Tsakiya, da suka dauki alhakin kai hare-hare kan Isra'ila a lokacin yakin Gaza.
Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jaddada wannan gargadin a wani jawabi da ya yi ta talabijin. Inda yace "Duk wanda ya illatasu, to zai ga mummunan sakamakon abin da ya yi.