Isra’ila ta kai wa Iran hari da makami mai linzami da sanyin safiyar Juma’a a cewar kafafen yada labaran Amurka.
Rahotanni da kafafen yada labarai na ABC, CBS da NPR suka fitar, ba su yi cikakken bayani kan inda makamin mai linzami ya hara ba.
Wani kakakin sojin Isra’ila ya ce ba zai ce komai ba “a yanzu” a lokacin da VOA ta nemi karin haske a wurinsa.
Kamfanin Dillancin Labaran Iran na IRNA, ya ce tuni hukumomin kasar suka dana makaman kare hare-hare a sararin samaniyar lardunan kasar da dama.
Kamfanin dillancin labaran na IRNA da kafar yada labaran kasar ta Iran Fars, wacce ke da alaka da dakarun juyin juya halin Islama, sun ce wata fashewa ta auku a Lardin Isfahan da ke tsakiyar kasar.
Harin na Isra’ila na zuwa ne kasa da mako guda bayan harin martani da Iran ta kai wa Isra’ila a ranar Lahadi da makamai da dama, wadanda Isra’ila ta ce ta kakkabo su tare da hadin gwiwar kawayenta.
Harin na ranar Lahadi martani ne kan harin da ake zargin Isra’ila ta kai ofishin jakadancin Iran da ke Syria, wanda ya halaka mutum bakwai ciki har da manyan hafsoshin sojin kasar biyu.
Da ma Isra’ila ta sha alwashin mayar da martani, yayin da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashe suke kira da a kai zuciya nesa don kada rikicin ya kazance.
Ita ma dai Iran ta sha alwashin mayar da zazzafan martani cikin gaggawa idan har Isra’ila ta kai mata hari.