Hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza da babban birnin kasar Lebanon sun kashe mutane da dama a ranar Alhamis, yayin da sojojin Isra’ila suka ce sun kai wa ‘yan ta’adda hari ne.
Jami’an lafiyar Falasdinawa sun ce hare-haren saman na Isra’ila sun fada kan wata makaranta a Gaza da ke zama mafaka ga mutane da suka rasa muhallansu suna masu cewa mutum 27 ne suka rasa rayukansu.
Isra’ila ta ce ta kai harin ne kan wata cibiyar da ake ba da umarni da ke cikin makarantar.
A babban birnin kasar Lebanon, Isra’ila ta kai hari a wani gini da ke tsakiyar birnin, mai nisa daga inda nan ne kungiyar Hezbollah ke da karfi sosai a kudancin birnin Beirut.
Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 22, yayin da 117 suka samu raunuka, amma ana fargabar za su karu yayin da masu aikin ceto suka maida hankali kan baraguzan ginin.