Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Fara Daukan Matakan Kwaso 'Yan Kasarta Daga Lebanon


Yadda hayaki yake tashi a wasu yankunan Beirut bayan da Isra'ila ta kai hari
Yadda hayaki yake tashi a wasu yankunan Beirut bayan da Isra'ila ta kai hari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Fara Shirin Kwaso mutanen da ke zama a kasar Lebanon, biyo bayan ta'azzarar rikici tsakanin Isra'ila da Iran.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman akan al’amuran kafafen sadarwa na zamani Dada Olusegun ne ya bayyana haka a ranar Talata sannan ya bukaci ‘yan Najeriya mazauna Lebann su tuntubi ofishin jakadancin don su ba da bayanan su.

A wani sakon da ya kafa a adireshin shafinsa na X @DOlusegun, mai bai wa shugaban shawara ya ja hankalin duk ‘yan Najeriya da ke Lebanon da “su tuntubi ofisihin jakadancin kasar don ba da bayanansu gabanin a fara kwashe su”.

A ranar Talata, Iran ta harba makamai masu linzami 180 cikin Isra’ila a matsayin martini akan kisan shugabanin Hezbollah.

Kasashen 2 sun yi ta barazana tsakanin su bayan ruwan makamai masu linzamin da Tehran tayi.

Firan ministan Isra’ila Beyamin Netanyahu, ya lashi takobi cewa, Isra’ila zata mai da martini mai zafi akan harin da aka kai mata.

A nasu bangaren kuma, kasar China da Saudi Arabiya sun yi kira da a kwantar da wannan tarzomar da take dada ruruwa a yankin Gabas ta tsakiya sannan, sun yi kira ga bangarorin biyu da su dawo kan teburin tattaunawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG