Isra’ila tace, zata bude sabuwar hanyar tsallakawa cikin Gaza domin ayyukan jin kai, a daidai lokacin da Amurka ke aza kaimin ganin an samar da Karin taimako ga Palasdinawan dake fama da karancin abinci da ta wurin zma, tun bayan barkewar yaki tskanin Isra’ila da Hamas.
Cikin wata sanarwar hadin guiwa a jiya Juma’a, rundunar dakarun Isra’ila da hukumar dake kula da aiyukan gwamnati a yankunan da ta mamaye, COGAT, sunce, ana shirye shiryen bude hanyar da ake cema Kissufim.
Sanarwar da aka saki ta kafar sadarwar zamani ta X tace, rundunar dakarun tsaron Isra’ila IDF da COGAT, na aiki ne bisa umurnin manyan shugabannin siyasa, a matsayin wani bangare na kokarin da akeyi na samar da Karin hanyoyin shiga ta tallafi cikin Gaza.
Sanarwar ta kara da cewa, dakarun tsaron Isra’ila sun gina cibiyoyin sa ido da samar da kariya akan hanyar Kissufim da ake tsallakawa, tare da samar da wasu hanyoyin a yankin Isra’ila da kuma a yankin Gaza domin bayar da damar shiga da tallafi yankin kudancin Gaza.
Kissufim wata karamar hanya ce da ake bi wajen tsallakawa cikin kudancin Gaza dake kusa da Kibbutz Kissufim, daya daga cikin yankunan da Hamas ta kaiwa hari a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2023, wani hari mai razanarwa da aka shammaci Isra’ila da shi, da ya haifar da yaki. Amurka, Birtaniya da sauran kasashen yammaci, sun Aiyana Hamas da Hezbollah dake Lebanon a matsayin kungiyoyin ta’addanci.
An dade ba’a amfani da hanyar, sai dai sojoji kawai, tun bayan da Isra’ila ta janye daga Gaza a shekarar 2005.
Sake bude hanyar yazo ne, yayinda wa’adin da sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken da sakataren ma’aikatar tsaron Amurka Lloyd Austin ke kusantowa. Cikin wata wasika da aka mika a ranar 13 ga watan Oktoba, Austin da Blinken sun ba Isra’ila kwanaki 30 da su inganta hanyoyin shigar da kayayyakin jin kai ga Palasdinawa a Gaza, ko ta fuskanci yuwuwar rage tallafin soji da Amurka ke bata.
Wasikar tayi kira ga Isra’ila da ta bada dama ga akalla manyan motocin daukar kaya 350 shiga Gaza a duk rana, ta hanyoyi hudu, ta kuma bude wata hanyar shiga ta 5.
A yayin wani jawabin ma’aikatar cikin gidan Amurka a ranar Alhamis, mai magana da yawun ma’aikatar Mattew Miller ya bayyana sabbin hanyoyin daya zayyana a matsayin kokarin Isra’ila na ganin ta samar da umurnin dake cikin wasikar. Miller yace, hakan ya hada da kokarin hana yin wasosos akan motocin dake dauke da kayayyakin agajin, da fadada yankin jin kai na Mawasi dake yankin Gaza.