Isra’ila Na Ci Gaba Da Gargadi Kan Falasdinawa Su Fice A Arewacin Gaza, Hamas Na Cewa Su Zauna

Yankin Zirin Gaza

Kakakin dakarun Isra’ila na zargin Hamas da yin amfani da fararen hula a matsayin makari, yana mai jan kunnen al’umar yankin da su tattara su koma kudancin Gaza. Amma Hamas ta ce duk farfaganda ne.

Falasdinawa na ci gaba da fadi tashin ficewa daga yankin arewacin Zirin Gaza yayin da Isra’ila ke ci gaba da kara fitar da sakonnin gargadi kan jama’a su fice a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP.

Ana tsammanin dakarun Isra’ilan na shirin kutsawa ne cikin yankin arewacin Gaza don fafatawa da mayakan Hamas.

Hakan na faruwa ne yayin da al’umar yankin Falasdinun ke fama da matsalar rashin ruwa bayan da Isra’ila ta datse hanyoyin samar da ababen more rayuwa a yankin.

Kakakin dakarun Isra’ila na zargin Hamas da yin amfani da fararen hula a matsayin makari, yana mai jan kunnen al’umar yankin da su tattara su koma kudancin Gaza.

A nata bangaren, ita ma Hamas tana kira ga jama’ar yankin da su zauna a gidajensu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kwararar jama’ar da yawanta ya kai miliyan 1.1 na jefa jama'a cikin mummunan yanayi.

A ranar 7 ga watan Oktoba Hamas ta kai harin cikin Isra'ila wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Isra'ila ta mayar da martani kan yankin Gaza, lamarin da shi ma ya yi sanadin mutuwar daruruwan Falasdinawa.