Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Ziyarar Ibada Urshalima


Mabiya addinin Kirista da suko dawa daga Isra’ila
Mabiya addinin Kirista da suko dawa daga Isra’ila

Gwamnatin ta Najeriya ta dakatar da Ziyarar ne har sai an samu salama, biyo bayan kaurewar fada tsakanin Falasdinawa ‘yan kungiyar Hamas da sojojin Isra’ila.

ABUJA, NIGERIA - Rukunin masu ziyarar ibadar na biyar a bana daga jihar Lagos da ke dauke da mutum 350 ya dawo gida lafiya bayan ziyartar sassan ibada yayin da a ke barin wuta a yankin Gaza.

Babban sakataren hukumar ziyarar ibadar Reverend Yakubu Pam ya ce kimanin mutum 50 ne daga Lagos ba su samu tafiya ba gabanin dakatar da ziyarar kuma za a koma tafiya da zarar salama ta samu.

Reverend Pam ya kara da cewa ziyarar kan shafi cikin Isra’ila da Jodan don haka masu ibadar su ka takaita ga arewacin Israila inda ba a arangama “wuraren da mu ke tafiya na ta arewa a Israila, kuma Allah ya sa rikici bai same su ba domin Gaza na da nisa daga inda su ke. Sun yi tafiyar su, sun duba wurare da za su yi ibadar su ba damuwa.”

Pastor Simon Dolly
Pastor Simon Dolly

A nasa sharhin kan fitinar ta Yahudawa da Falasdinwa sakataren kungiyar Kiristoci reshen arewa ta tsakiya Simon A.S Dolly ya ce cika alkwarin manzanci ne a littafi mai tsarki da ke bukatar neman sauki daga Allah.

A gefe guda malaman Islama na kira ga samun adalci a matsayin hanyar kawo karshen fitinar ta shekaru aru-aru.

Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya ce fitina ba ta kawo wata riba ga jama’ar da ke zaune a yanki daya “mu na kira ga jama’a a cigaba da tayawa da addu’a don samun zaman lafiya.”

Prof. Mansur Sokoto
Prof. Mansur Sokoto

Kamar yanda Saudiyya ke da muhimmanci ga al’ummar Najeriya musamman Musulmi don aikin hajji, hakanan yankunan Israila da Falasdinawa ya ke ga Musulmi, Kirista da ma masu wata akidar da ta saba da wadannan don masallacin Baitul Mukaddas da ke da daraja ga Musulmi, Kirista da Yahudawa.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Ziyarar Ibada Urshalima .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG