Manyan jigajigan jam'iyyu irin su PDP da APC sun soma furta ra'ayoyinsu kan irin dan takarar da suke ganin zai zaben 2015 ya shugabanci kasar.
WASHINGTON D.C. —
Manyan jam'iyyu irin su PDP da APC sun soma bayyana ra'ayoyinsu kan irin nau'in dan takarar da suke gani zai iya basu kujerar shugaban kasa a zaben 2015.
Wannan tunanen ya biyo bayan ra'ayin Majalisar Dattawan Arewa ne a karkashin Alhaji Tanko Yakasai dake muba'aya da cigaban mulkin shugaba Jonathan amma da mataimakinsa Alhaji Namadi Sambo. Tsohon dan siyasa Tanko Yakasai yana ganin yunkurin zai kawo hadin kan 'yan Najeriya. A furucin da ya yi Tanko Yakasai yace "Ban saci kayan kowa ba amma yau shekara 61 da ta wuce aka kamani aka daureni a Kano saboda nayi zanga zanga a filin jirgin sama kan goyon bayan hadin kan Najeriya. Akwai 'yan arewa da yawa da suka sha wahala a kan hadin kan Najeriya. Har ta kai ana kiranmu nyamuran arewa muka jimre amma Allah Ya sa bani ba kowa ma wanda yake arewa yana jin dadin Najeriya. Ka taba jin dan arewa ko dan Najeriya yana tallar ruwa a Niger?"
Suma masu rajin mulki ya dawo arewa amma ba lalle a hannun Janaral Buhari ba sun fara ambata dalilai. Alhaji Adamu Abubakar shugaban karamar hukumar Maigatari a jihar Jigawa da yake furuci kan Janaral Buhari sai yace "Mutumin da ake ganinsa janaral yayi yaki ya kai shekara talatin da wani abu ko arba'in yana soja, kawai rana tsaka yanzu shi ake dauka ya fi kowa iya siyasa shi ne ma janarar 'yan siyasa. A zato ko hange kawai shi ne ya fi kowa iya abu kuma bashi da ilimin abu. Siyasar Najeriya ma zan iya cewa ta sha giya ta sha kwaya. Babu mutumin da zai ce a aikin soja bai san abun da ake kira janaral ba amma yadda aka kambamashi, ai ban manta ba da wayo na da hankalina Buhari din nan shi ne yake cewa 'yan siyasa barayi ne saboda haka shi ba ma zai shiga siyasa ba. Ka ga waccan kalma idan ka kwatanta akwai ilimi na siyasa ke nan?"
To amma ga Sanato Hadi Sirika wanda yace bayan aikata gaskiya da rikon amana irin Muhammed Buhari hatta mulkin da yayi ya fi tasiri ga nau'in mulkin farar hula da a keyi yanzu. Yace "had dai in ka zabi mutumin kwarai ka yi tsamnani zai yi abun kwarai kuma wani da ance wani ne ke mulki ko bai dauka kara ba za'a bi layi kuma a Najeriyar nan an yi mun gani. Kuma ba tsawon dadewa ba ne ke janyo cigaba ba...An yi gwamnatoci da dama amma gwamnatin da aka fi tunawa a Najeriya ita ce gwamnatin Murtala Muhammed da gwamnatin Janaral Buhari. Kuma dukansu su ne mafi karancin dadewa a mulki. Murtala Muhammed kwanashi dari biyu kurum shi kuma Janaral Buhari shekara daya yayi kawai da wata takwas. Amma an fi tunawa da gwamnatinsu. Ta fi yiwa talaka anfani. Ta fi kare mutuncin Najeriya da lafiyar 'ya'yanta da lafiyar dukiyarsu da lafiyar ita kanta kasar. Al'umma su gane cewa idan zabe ya dawo 2015 dole su zabi mutanen kwarai wadanda ko basu daga kara ba za'a kallesu a yi koyi dasu.
Alamu na nunawa cewa talakokin arewa masu kada kuri'a suna marawa Janaral Buhari baya ne domin idan za'a tuna a zaben 2011 ya lashe kuri'u miliyan 12 a fadin kasar.

Your browser doesn’t support HTML5