Ko yija sai da hukumomin 'yan sanda suka fafata da 'yan fashi da makami a jihohin Bauchi da Gombe kamar yadda hukumomin 'yansandan suka sanar.'Yan sandan sun fafata da 'yan gungun fashi da makami da ya jawo asarar rayuka har bakwai. Wadanda suka rasu sun hada da 'yan banga masu gadin gidan mai a Bauchi.
Kakakin 'yan sanda a jihar Bauchi DSP Haruna Muhammed ya ce 'yan fashin sun kai hari a kan wani gidan mai a Yankari inda suka sassari 'yan banga biyu dake gadi a wurin wadanda daga bisani sun rasu. Su 'yan fashin sun sake shiga wani gidan mai a nan Yankarin inda suka jima masu gadi biyu ciwo. Sun saci naurori masu kwakwalwa biyu. A hanyar Soro a wani gari Kafin Rabi barayi shida sun tare hanya suna kwanta kwanta a wurin. Nan 'yan sanda da wasu 'yan banga suka samesu suka fafata. 'Yan sanda sun kashe daya kana sun kama daya wanda yanzu yana taimakawa 'yan sanda wajen bincike.
Haka ma tsakanin Soro da Darazo akwai wani wurin da barayi suka fake. 'Yan sanda sun je sun samu harsashen bindigogi kirar A47 da ake kira magazine guda ashirin da biyu da rigunan 'yan sanda da kuma irin tarhon da 'yan sanda ke magana da shi da kuma wasu kaya amma mutanen sun gundu.
A jihar Gombe shahararren mai yaki da 'yan fashi da makami Ali Kwara ya ce sun samu labari cewa wasu barayi daga kudancin kasar da 'yan arewa daga Kano da suka girma a kudu suka hada karfi suka tashi cikin motoci uku zasu kai hari kan kamfanin siminti dake Ashaka. Ya ce an basu lambobin motoci biyu na ukun ne basu samu ba. Barayin zasu bi hanyar Dukku su kai inda suka nufa. Shi Ali Kwara da 'yan sanda suka shirya domin su cafkesu kuma an ci nasarar makasu.