Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Gombe ta Koma Baya – inji Danjuma Goje


Senata Muhammadu Danjuma Goje
Senata Muhammadu Danjuma Goje

A karshen makonnan ne, jam’iyyar APC mai adawa ta jihar Gombe ta shirya gangami inda tsohon gwamnan jihar wanta a halinyanzu Senata ne a majalisar dattijan Najeriya, Alhaji Mohammadu Danjuma Goje ya soki gwamnatin PDP mai mulkin jihar da janyo koma baya a cikin jihar.

Ita kuma jam’iyyar PDP ta gudanar da taron ‘yan jarida, domin mayar da martani. Wani mai taimaka wa Gwamnan jihar, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, Umar Muazu ya mayar da martani.

Mr. Muazu yace “wannan taron ‘yan jarida da muka kira, don mu mayar da martani ga tsohon gwamnan jihar Gombe, Muhammad Danjuma Goje. Na farko, maganar babu kudi, muna so mu tabbatar ma jama’ar Najeriya ba wai jihar Gombe kawai ba, akwai kudin da ake amfani da su ana aiki da su. Sauran kudin da yake cewa babu kuma mu a namu takardun, gwamnatinsa daga 2003 zuwa 2011 ya sauka, akwai kudaden da muke nema da dama a wajensa, wanda yanzu muna so hukumar EFCC ta karbo, don mu cigaba da yiwa jama’a aiki”.

Wadannan kalamu sun biyo Danjuma Goje ne bayan sukar jam’iyyar PDP a jihar da yayi, inda yace gwamnatin jihar bata cikawa jama’a alkawuransu ba, kuma fatara ya dame su, kuma ba’a biyan ma’aikatan gwamnati albashi, kuma jihar ta koma baya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG