Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa Mai Mala Buni ya ce duk da bita da kulin da wasu da basu da kishin jihar su keyi jam'iyyar sai kara karfi ta keyi musamman domin hadewar da aka yi. Ya ce dama can ANPP ke rike da jihar yanzu da ANPP ta narke cikin APC karuwa suka yi. Mutanen jihar sun amince da gwamnan Alhaji Ibrahim Geidam domin rikon amana da yake da shi. Gwamnan na tafiyar da gaskiya a cikin mulkinsa. Talakawa sun gamsu da aikin gwamnan. Ya ce a yankinsu a jihar Yobe ce kawai 'yan majalisa dari bisa dari 'yan APC ne. A majalisar dattawa duk sanatocin uku 'yan APC ne domin haka jam'iyyar bata da baraka a jihar Yobe.
Al'ummomin jihar sun fadi albarkacin bakinsu kan jiharsu.Wani Ibrahim Bala Abubakar ya ce karamin ministan kudi ya ce babu tsaro a jihar amma an yi zaben kananan hukumomi lafiya kana shi ministan yanzu wai yana rangadin jihar idan babu tsaro yaya aka yi yana rangadi. Ya gargadi ministan ya daina yiwa jihar Yobe shishigi kana ya roki gwamnan Ibrahim Geidam ya yi hakuri da kalaman da aka yi masa na batanci. Shi Sale Bakoro shugaban kungiyar talakawa ya ce yana kiran mutane lokacin zabe su yi la'akari da gwamnatin da ta yi musu aiki. Ya ce su guji wadanda suke Abuja domin suna da mukami amma wadanda basu damu da jihar ba sai lokacin zabe su zagayo suna cewa su 'ya'yan jihar ne.