Fadar shugaban Amurka ta White House ta fada wa Muryar Amurka cewa ta girgiza da jin rahotannin da ba’a tabbatar da su ba daga yammacin duniya cewa, Iran ta kai wa Rasha makamai don amfani da su a kan Ukraine ko kuma za ta kai a kwanan nan.
Iran ta mai da martani kan wadannan rahotannin ta hanyar shaida wa Muryar Amurka a kebance cewa, ta kaurace wa samar da makamai ga bangarorin da ke cikin yakin da kawarta Rasha ta kaddamar kan Ukraine.
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito a jiya Juma'a cewa, wani jami’in Amurka da na Turai da ba’a bayyana sunayensu ba, sun tabbatar da cewa a ‘yan kwanakin nan Iran ta ba da makamai masu linzami ga Rasha, a karkashin wani shiri da zai zama na farko na habakar kawancen soji tsakanin kawayen kasashen 2 masu adawa da yammaci.
Kafin labarin na jaridar, kafafen Bloomberg da Reuters sun wallafa rahotannin a ranar Litinin da kuma ranar 10 ga watan Agusta, suna masu hakaito wasu jami’an turai da ke cewa babu ko shakku kan makaman da Iran ta turawa Rasha.
Muryar Amurka ta bukaci kwamitin tsaron kasa na fadar White House a jiya Juma'a, da ya tabbatar da ko an riga an mika makaman ko kuma har yanzu ana kan niyya, kamar yadda kafafen yada labaran na yammacin duniya suka ruwaito.
Kakakin kwamitin tsaron Sean Savett, ya mayar da martani da wata sanarwa inda ya ce Amurka ta girgiza da jin wadannan rahotannin.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito wasu jami'an leken asiri na turai guda biyu suna cewa mika makaman zai hada da makamai masu linzami na Iran kirar Fath-360 da Ababil, wadanda dukkansu an ware su a matsayin makamai masu linzami da ke cin dogon zango har kilomita 300.
Irin wadannan makamai masu linzami na Iran za su iya ceto tarin makamai masu linzami na Rasha don kai hare-hare masu nisa zuwa Ukraine.