Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man Fetur Din Dangote Zai Fara Isa Kasuwa Makon Gobe – NNPCL


Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)
Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)

Kamfanin man fetur din Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa man fetur din matatar Dangote zai fara isa kasuwa tun daga ranar 15 ga watan Satumba mai kamawa.

Kamfanin wanda ya bayyana hakan a sanarwar da babban jami’in yada labaransa, Olufemi Soneye ya fitar a jiya Alhamis a Abuja, tace kasuwa da kanta ce zata yanke farashin da za a sayar da man.

Hakan dai ya biyo bayan fara tace man fetur din da matatar ta Dangote tayi a farkon makon nan.

Da yake ruwaito kalaman mataimakin shugaban bangaren cinikayyar albarkatun man kamfanin NNPCL, Adedapo Segun, Soneye yace an kammala cefanar da bangaren cinikayyar kamfanin don haka bashi da sauran hakkin yanke farashi.

Kalaman nasa sun kawo karshen rade-raden da ake yi na cewar NNPCL zai cigaba da yanke farashin albarkatun man fetur.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG