Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Daure ‘Yan Najeriya 2 Bayan Damfarar Ba'Amurke Da Ya Kashe Kansa


Samson da Samuel Ogoshi
Samson da Samuel Ogoshi

Wadanda suka zambatar sun hada da wani matashi dan shekara 17, Jordan Demay, daga jihar Michigan wanda ya hallaka kan sa da kan sa.

An daure ‘yan Najeriyar 2, wa da kani shekaru 17 da rabi a gidan kaso bayan da suka amsa laifin yin yaudara ta hanyar lalata a intanet da matasa maza a fadin Amurka.

Wadanda suka zambatar sun hada da wani matashi dan shekara 17, Jordan Demay, daga jihar Michigan wanda ya hallaka kan sa da kan sa.

A jiya Alhamis, wani alkalin kotun tarayya ya yankewa Samuel Ogoshi mai shekaru 24 da kaninsa Samson Ogoshi dan shekara 21 hukunci bayan daya saurari bayanai masu ban tausayi daga iyaye da matar uban Jordan Demay.

Jordan DeMay(DeMay family
Jordan DeMay(DeMay family

Jordan Demay nada shekaru 17 da haihuwa sa’ilin daya hallaka kansa a gidansu dake garin marquette na jihar michigan.

Ana zargin ‘yan Najeriyar 2; Samuel da Samson Ogoshi da gudanar da wata kungiyar zambar-lalata ta kasa da kasa daga Najeriya ta hanyar gabatar da kansu a matsayin mata tare da zambatar wadanda suka fada hannunsu su aiko musu da hotunansu na batsa.

Jordan DeMay(DeMay family
Jordan DeMay(DeMay family

Bisa ga jami’ai, Samuel Ogoshi ya yi amfani da shafin sada zumunta mai suna dani.robertts a ranar 25 ga watan Maris 2022, bayan da suka rudi DeMay ya tura masu hotonshi tsirara, sannan ya yi masa barazana don ya biya toshiya.

A hirar ta da tashar talabijin ta TV6 mahaifiyar DeMay ta ce bata taba yin tsammanin hukumomi za su iya kamowa da kuma hukumta wadanda su ka yi sanadin mutuwar danta ba, ta ce, hukumomi sun yi daidai da suka tasa keyarsu zuwa Amurka domin amsa laifinsu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG