Iran Ta Sanar Da Sake Bude Ofishin Diflomasiyya a Saudiyya

Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da China da kuma Saudiyya.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa za ta sake bude ofisoshin diflomasiyya a kasar Saudiyya a cikin wannan mako, tare da maido da huldar diflomasiyya bayan da aka shafe shekaru bakwai ana takaddama a kai, kamar yadda kafar yada labarai ta kasar ta rawaito a ranar Litinin.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kanaani ya bayyana cewa, a ranakun Talata da Laraba ne za a bude ofishin jakadancin Iran a Riyadh da karamin ofishin jakadancinta a Jeddah, da kuma ofishin dindindin na kungiyar hadin kan kasashen musulmi.

A watan Maris, Iran da Saudi Arabiya sun amince da kulla huldar diflomasiyya, a wata yarjejeniya da China ta samar, wadda ke wakiltar wani babban ci gaba a yankin.

A shekarar 2016 ne Saudiyya ta katse hulda da Iran bayan da masu zanga-zangar suka mamaye ofisoshin diflomasiyya na Saudiyya a Tehran, da kuma birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin kasar a lokacin zanga-zangar da ta haifar da kisan wani fitaccen malamin Shi'a da wasu 46 a masarautar mai arzikin man fetur.

Kanaani ya kara da cewa ofishin jakadancin Iran da ke Riyadh da karamin ofishin jakadancinta a Jeddah, tuni suka fara gudanar da ayyukanta na taimakawa alhazan Iran da ke zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajji a karshen watan Yuni.