Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Daular Larabawa Ya Nada Dansa A Matsayin Yarima Mai Jiran Gado


FILE - Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan.
FILE - Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan.

Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan ya nada babban dansa Sheikh Khaled a matsayin yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, babban birnin kasar mai arzikin man fetur a yankin Gulf, tare da nada 'yan uwansa a kan manyan mukamai.

Sheikh Mohammed, wanda ya zama shugaban kasa kuma mai mulkin Abu Dhabi a bara bayan ya jagoranci kungiyar OPEC da ke kawance da Amurka tsawon shekaru, ya nada dan uwansa Sheikh Mansour a matsayin mataimakin shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum.

Wannan ya bayyana kara mamaye mulki a Abu Dhabi, wanda shine hedkwatar siyasa ta Tarayyar Hadaddiyar Daular Larabawa ta masarautu bakwai, saboda dimbin arzikin mai. Dubai ita ce cibiyar kasuwanci da yawon bude ido ta Tekun Fasha.

Sheikh Mohammed ya nada 'yan uwansa Sheikh Tahnoun bin Zayed Al Nahyan da Hazza bin Zayed Al Nahyan a matsayin mataimakan sarakunan Abu Dhabi. Sheikh Tahnoun kuma shi ne mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa kuma yana kula da daular kasuwanci mai fadada.

FILE - Sheikh Khaled bin Mohamed bin Zayed Al Nahyan Yarima Mai Jiran Gado.
FILE - Sheikh Khaled bin Mohamed bin Zayed Al Nahyan Yarima Mai Jiran Gado.

Ta hanyar nada fitattun 'yan uwa sabbin mukamai, ya kiyaye "wasu ma'auni na raba madafun iko, amma a cikin dangin [Abu Dhabi] Al Nahyan kawai," a cewar Cinzia Bianco, jami'ar bincike a Majalisar Turai kan Harkokin Waje, ta kafar Tuwita.

Zabin Sheikh Khaled a matsayin yarima mai jiran gado yana nuna yanayin da ake ciki a yawancin masarautun Larabawa na yankin Gulf zuwa zuriyar kai tsaye - 'ya'ya fiye da 'yan'uwa - don maye gurbinsa, gami da na Saudi Arabiya.

Abu Dhabi dai ya rike shugabancin kasar ne tun bayan kafa kungiyar hadaddiyar daular Larabawa da mahaifin Sheikh Mohammed ya kafa a shekarar 1971.

Sheikh Mohammed, wanda aka fi sani da MbZ, ya kasance yana horar da dansa a fannin tsaro - ciki har da leken asiri - tattalin arziki da mulki, in ji manazarta.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ne ya rawaito labarin.

XS
SM
MD
LG