IRAN: An Cimma Yarjejeniya Akan Shirin Nukiliya da Kasashen Duniya

Wani kwararre yake aiki a wata masana'anatar tace Uranium na Iran.

Manyan kasashen duniya sun cimma yarjejenia da Iran wadda zata takaita shirin makaman nukiliyar ita Iran din don neman sassucin takunkuman tattalin arziki da aka sa mata, abinda kuma ya kawo karshen zaman da aka kwashe shekaru goma ana shawarwari masu zafi.

Shugaba Obama ya fadi cewa wannan yarjejeniyar ta nuna cewa diplomasiyyar Amurka zata iya kawo kyakkyawan chanji.

Shugaba Obama ya kara da cewa “an kulla cikakkiyar yarjejeniya, ta lokaci mai tsawo da Iran, wadda zata hana kasar yin makaman nukiliya. Ya kuma ce zai yi amfani da karfin ikon sa wajen soke duk wani shirin doka da majalisar Amurka da zata gabatar don toshe yarjejeniyar.

Shugaba Obama yayi wannan bayanin ne jim kadan bayan da shugabar hukumar kula da harkokin wajen tarayyar turai Federica Mogherini da ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif suka bada sanarwar kulla yarjejeniyar a Vienna, biyo bayan makonni biyu da aka kwashe ana ganawa dare-da-rana don fidda abubuwan da yarjejeniyar zata kunsa, yadda za a takaita shirin makaman nukiliyar Iran da kuma neman sa ido daga cibiyar dake kula da harkokin nukiliya a Majalisar Dinkin Duniya.

Mogherini ta fadi cewa yarjejeniyar ta sami daidaituwa ta kuma mutunta muradan duka sassan da suka gana.

Bayan da ta gama Magana a Vienna, ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif shima ya yi wa manema labarai bayani a Persia, inda ya maimaita abinda Mogherini ta fada.