Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN), ta ayyana cewar zata rufe gidajen mai dubu 30 da mambobinta ke gudanarwa a fadin kasar nan matukar gwamnatin tarayya ta gaza biyan bashin Naira bilyan 200 da take binta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewar, Hukumar Dake Kula da Kasuwancin Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) wacce mallakin gwamnatin tarayya ce, ta gaza biyan bashin, wanda ya cigaba da taruwa tun cikin watan Satumbar shekarar 2022.
IPMAN nada iko da fiye da gidajen mai dubu 30 a fadin najeriya.
Hakkokin tura mai wasu kudade ne da gwamnati ke biyan dillalan mai saboda safarar albarkatun man fetur din da aka loda daga rumbunan adana man zuwa jihohin dake fadin kasar nan.
A cewar Alhassan, sakamakon gaza biyan bashin naira bilyan 200 daga bangaren Hukumar NMDPRA ba zai zamo mai kyau ba, kasancewar za'a rufe dukkanin gidajen man dake fadin Najeriya.
Alhassan ya kara da cewar, "a matsayinmu na IPMAN, mun dauki dukkanin matakai a baya domin kaucewa fadawa cikin wannan mummunan al'amari, wanda muka tabbatar ba zai yiwa 'yan Najeriya dadi ba, amma yanzu bamu da wani zabi illa mu fito kwanmu da kwarkwata domin magance wannan matsala ta hanyar da muka fi ganin ta dace, wanda hakan ka iya sake 'yan Najeriya cikin halin kunci da wahala.