Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Karancin Man Fetur Ta Kawo Cikas Ga Harkokin Jama’a A Kano


Karancin man fetur a Najeriya, mutane na layi
Karancin man fetur a Najeriya, mutane na layi

Karanci da tsadar man fetur na ci gaba da barazana ga harkokin yau da kullum a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman a manyan biranen kasar. Kano na daga cikin wuraren da wannan matsala ke kawo cikas ga jama'a, inda ake sayar da lita daya ta mai daga naira dari tara da hamsin zuwa dubu daya.

Malam Sanusi Abdul’aziz, matukin babur din adaidaita sahu ne, ya ce tun da asuba ya fita neman man fetur amma har bayan karfe 12 na ranar Talata bai san makomarsa ba, kuma bai sami damar zuwa wurin sana'arsa ba.

Shi kuwa Malam Rabi’u Yahaya, da shi ma ya yi sammakon zuwa sayen man, ya ce tun jiya yake kokarin samun man amma har yanzu bai sami hali ba.

Bayan ‘yan kasuwa da masu ababen hawa na haya, matsalar ta jefa daliban da ke zuwa makaranta cikin garari, kamar yadda Musa Habibu ya shaida.

Alhaji Mansur Tanimu, Shugaban kungiyar mammalaka da matukan baburan adaidaita sahu a Kano, ya ce lamarin ya baci, yanzu har ta kai ga wasu masu ababen hawa na adaidaita sahu na ajiye su saboda ko da sun sayi man babu riba.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum irinsu Kwamred Yahaya Shu’aibu Ungogo, ya ce gwamnati ce ta kyale dillalan man fetur suna cin karensu babu babbaka, amma idan gwamnati ta yi tsayin daka za a gyara lamarin.

Lokuta da yawa dai kungiyar IPMAN ta sha fadin cewa bata da iko ko zarafin yin wani abu a irin wannan yanayi, lamarin da Kwamred Ungogo ya ce ya kamata gwamnati ta tashi tsayi.

Nan take dai kungiyar IPMNAN ta jihar Kano ba ce komai ba game da batun.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Matsalar Karancin Man Fetur Ta Kawo Cikas Ga Harkokin Jama’a A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG