Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Karin Kashi 35% A Albashin Ma'aikatan Gwamnati


Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, Abuja
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, Abuja

A ranar Talata ne Najeriya ta kara wa ma’aikatan gwamnati albashi da kashi 25% zuwa 35%, tun daga watan Janairu da ya gabata, in ji hukumar albashi, yayin da kasar mai mafi girman tattalin arziki a Afirka ke fama da matsalar tsadar rayuwa na kusan shekaru talatin.

WASHINGTON, D. C. - Ma’aikacin gwamnati mai mafi karancin albashi zai rika samun Naira 450,000 a shekara, kwatankwacin dalar Amurka 323.97 ko kuma 37,500 a duk wata, in ji Hukumar Samar da Albashi, da Kudaden Shiga da Hakkokin Ma’aikata Ta Kasa.

Karin albashin ya shafi dukkan ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka hada da na bangaren lafiya, ilimi da tsaro.

Gwamnati na tattaunawa daban-daban da kungiyoyin kwadago a kan sabon mafi karancin albashi na wata-wata na kasa, wanda tun a 2019 aka yi nazarinsa na karshe.

‘Yan Najeriya dai na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki da kashi 33.20%, wanda shi ne mafi tsanani a cikin shekaru 28 da suka gabata, bayan da gwamnati ta cire tallafin man fetur ta kuma daina daidaita darajar kudaden kasashen waje, lamarin da ya durkusar da darajar Naira.

Hukumar kula da wutar lantarki ta kasar kuma a wannan watan ta kara kudin wuta ga wasu masu amfani da wutar lantarki a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin yaye tattalin arzikin kasar daga tallafin da take bayarwa domin rage yawan dogaro ga kudaden gwamnati.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG